Dakarun Faransa na luguden wuta a Gao

sojin Faransa
Image caption Sojin saman Faransa a Mali

Sojojin saman Faransa sun fadada luguden wutar da suke yiwa 'yan tawayen kasar Mali, inda su ka yi ruwan bama-bamai a bisa garin Gao, wanda ke karkashin ikon 'yan tawaye a arewacin kasar.

Ministan tsaron Faransa ya ce jiragen yakinsu sun kai hari kan sansanonin horar da mayaka da kuma kayayyakin more rayuwa.

Yace "yanzu haka ana luguden wuta. Da yamma ma za'a kuma haka ma gobe. Shugaban kasa ya riga ya sha alwashi; wajibi ne mu kai da 'yan ta'adda wadanda ka iya barazana ga Mali, da kasarmu da ma nahiyar Turai baki daya."

Mazaunan Gao sun ce 'yan tawaye da dama sun kauracewa garin.

Daruruwan dakaru daga kasashen yammacin Afrika na shirin kai dauki kasar ta Mali.

Burtaniya ma ta bada jiragen sufurin soji guda biyu domin jigilar makamai da sojojin Faransa.

Karin bayani