Isra'ila na wariyar jinsi! Inji Barghouthi

Dakarun Isra'ila sun kori masu fafutukar Palasdinu da na kasashen waje daga wani sansanin kan tsauni a gabar yammacin kogin jordan.

Fitaccen dan siyasar Palasdinu din nan, Mustafa Barghouthi na daga cikin wadanda 'yan sanda suka kora a da tsakar daren jiya.

Yace wannan tsarin wariyar jinsi ne. Su na barin Yahudawa 'yan kama-wuri zauna su yi kaka-gida a wannan yanki da suka sata, sannan kuma su na cafke mu Palasdinawan da mu ke bin hanyar lalama wurin nuna rashin amincewa da a kwace mana filayenmu.

Kafa sansanin dai wata sabuwar dabara ce da Palasdinawa suka koya daga Yahudawan Isra'ila 'yan kama-wuri-zauna.

Palasdinawan sun kafa sansanin domin nuna rashin amincewarsu da gina wata unguwar Yahudawa, da za ta raba Palasdinawa da birnin Qudus.

Majalisar dinkin duniya dai ta haramtawa Isra'ila gina sansanonin Yahudawa a gabar yammacin kogin Jordan sai dai Isra'ila ta dade ta na yiwa wannan hukuncin kunnen kashi.

Karin bayani