'Farmakin sojojin faransa na tasiri a Mali'

Dakarun kasar Faransa a Mali
Image caption Dakarun kasar Faransa a Mali

Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius ya ce farmakin da sojojin Faransa ke kaiwa kan 'yan tawayen Mali na tasiri.

Mr. Fabius ya kara da cewa, cikin 'yan makonni masu zuwa za a dakatar da tsoma bakin sojojin Faransa kai tsaye a kasar ta Mali.

Mayakan saman Faransar na kara fadada ruwan bama-baman da suke yi wa 'yan tawayen a arewa maso gabashin kasar, inda suke kai hari a kan sansanonin horar wa da ajiye makamai a garuwuwan Gao da Kidal, inda 'yan tawayen suka fi karfi.

Mazauna garin na Gao sun ce 'yan tawayen da dama sun arce daga garin.

Lokacin da yake magana a gidan radio da talabijin na Faransa, ministan ya ce lokacin da 'yan tawayen suka yanke shawarar yin fito na fito, ya kasance batu ne na ko a mutu ko a yi rai.

Ya kara da cewa shigar da kasar Faransar ta yi cikin fadan na kasar ta Mali, zai kasance na dan kankanin lokaci ne, don basu da aniyar kasancewa a cikin kasar na dundundun.''

Nan gaba a yau ne, Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai tattauna a kan fadan da ake ci gaba da gwabzawa a Mali.

Yanzu haka daruruwan sojoji daga makwabtan kasashen yammacin Afrika, suna shirye-shiryen zuwa kasar ta Mali, don shiga yakin.