Faransa ta yi kira ga kasashen duniya

Dakarun sojin Faransa a Mali
Image caption Dakarun sojin Faransa a Mali

Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius, ya bukaci kasashen duniya da su goyi bayan matakin sojin da ake dauka kan 'yan tawaye a kasar Mali.

Mr Fabius ya ce Faransa ba za ta bari Mali ta zamo tudun mun tsira ga 'yan ta'adda ba.

A daidai lokacin da kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniya ke shirin zama domin tattauna batun na Mali, Mr Fabius ya jaddada cewa kasarsa ba za ta dauki nauyin batun tsaro ita kadai a Mali ba.

Ministan harkokin wajen Mali Tieman Hubert Coulibaly, ya ce batun ba na dakatar da 'yan tawaye ba ne kawai.

Can a fagen daga kuma, mayakan Islamar sun kwace iko da garin Diabaly a tsakiyar kasar daga hannun dakarun gwamnati.

Sai dai gwamnatin Faransa ta ce hare-haren da jiragen yakinta ke kaiwa ya sa 'yan tawayen sun ja baya a Kudancin kasar.

Karin bayani