An yankewa Ahmed el Gizawy hukunci

Shari'ah
Image caption An yiwa Ahmed el Gizawy shari'ah

Tsohon lauyan wani mai kare hakkin bil'adama na kasar Masar, da aka zarga da safarar miyagun kwayoyi a Saudi Arabia, ya ce an yanke masa hakuncin shekaru biyar a gidan yari da kuma bulala dari uku.

Batun na Ahmed el Gizawy ya haifar da rikicin diplomasiyya tsakanin Masar da Saudiyya, bayan da aka kama shi a watan Afrilun da ya gabata, lokacin da ya je Saudiyya domin aikin hajji.

Hukumomin Saudiyya sun ce an kama shi da dubban miyagun kwayoyin da aka haramta.

Sai dai magoya bayansa sun ce kaman na da nasaba da aikace-aikacen da yake yi a madadin 'yan kasar ta Masar da ake tsare da su a Saudiyya.

Karin bayani