Haramtaccen kasuwancin hauren giwa a Najeriya

Image caption Taswirar Najeriya

Masu yaki da haramtaccen kasuwanci a Najeriya sun ce har yanzu ana ci gaba da kasuwancin hauren giwaye ba bisa ka'ida ba duk da kokarin da gwamnati ke yi na magance hakan.

Masu kare gandun daji da suka gudanar da bincike a wata babbar kasuwa a Legas, sun shaidawa BBC cewa an yi cinikin hauren giwaye 14,000 ba bisa ka'ida ba a bana, wanda hakan ya ninka sau uku kan cinikin da aka yi a binciken da suka gudanar a shekaru goma da suka gabata.

Wani dan jarida daga sashen China na BBC wanda ya yi sojan-gona ya ce an ba shi fiye da kilogiram dari daya na hauren giwa.

Masu kare gandun daji sun ce bunkasar tattalin arzikin China na daga cikin abubuwan da ke sanya wa ake yawan samun masu bukatar hauren giwa.

Karin bayani