Tallauci ya ɗan ragu a Najeriya- Bankin duniya

Wani kauye a Arewacin Najeriya
Image caption Tallauci ya fi ƙamari a Arewacin Najeriya

Wani binciken da bankin duniya ya gudanar ya nuna cewa har yanzu al'ummar Najeriya na fama da talauci.

Sai dai binciken ya ce kaifin talaucin ya ragu, amma raguwar ba ta taka kara ta karya ba.

Mataimakin shugaban bankin mai kula da nahiyar Afirka ne, Makhtar Diop ya bayyana haka, lokacin da ya gana da shugaban Najeriya, Dr Goodluck Jonathan a Abuja.

Gwamnatoci daban-daban a Najeriyar dai kama daga jihohi zuwa matakin Tarayya sun sha fito da shirye-shirye a lokuta daban-daban da nufin yaƙi da tallauci, amma da dama ba su raka ba, sakamakon zargin da ake yi cewa son kai da na zuciya da kuma cin hanci da rashawa ne suka durkusar da su.

Sai dai Mr Diop ya jinjina wa Najeriya bisa karfin da tattalin arzikinta ya yi a lokacin da tattalin arzikin manyan kasashen duniya ke fuskantar koma baya.

Karin bayani