An bada sammacin kame Fira ministan Pakistan

Raja Pervez Ashraf
Image caption Ana zargin Raja Pervez Ashraf da cin hanci

Kotun kolin Pakistan ta bayar da sammacin kame Fira ministan kasar Raja Pervez Ashraf, bisa zargin cin hanci da rashawa.

Ana zargin Mr Ashraf da wasu jami'ai 15, da karbar na-goro a hannun wani kamfanin wutar lantarki mai zaman kansa, lokacin da Mr. Ashraf din ke rike da mukamin ministan wutan lantarki.

Umarnin na zuwa ne a lokacin da dubban masu zanga-zangar adawa da cin hanci ke ci gaba da maci a Islamabad babban birnin kasar, su na masu kira ga gwamnatin da ta yi murabus.

Kuma wannan yasa 'yan sanda yin harbi a iska

Ana gudanar da zanga-zangar ne karkashin jagorancin fitaccen malamin addinin musulunci Tahir-ul Qadri.

Masu gangamin sun kaure da murna lokacin da suka ji labarin sammacin kame Fira ministan.

Karin bayani