An sace 'yan ƙasashen waje da dama a Algeria

Masana'antar haƙar iskar gas a Algeria
Image caption Algeria na haƙo iskar gas ne tare da wasu ƙasashen waje

Rahotanni daga Algeria sun ce 'yan bindigar da ake alaƙantawa da masu kishin Islama sun kai hari tare da mamaye wata cibiyar haƙar gas a Kudancin ƙasar inda suka yi garkuwa da 'yan ƙasashen waje da dama.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasar ta Algeria, ya ce an kashe 'yan ƙasashen wajen biyu.

An rawaito cewa jami'an tsaron Algeria sun yiwa wurin ƙawanya, inda kamfanin mai na BP da na Algeria da kuma Statoil na Norway ke aiki.

Shugaban kamfanin Statoil Lars Christian Bacher, ya ce lamarin ya ritsa da ma'aikatansa 17.

Wata sanarwa da aka ce ta fito daga wata ƙungiya mai alaƙa da Al-Qaeda, ta ce tana tsare da mutane 41.

Sannan ta ce ta kai harin ne saboda goyon bayan da Algeria ke bayarwa ga matakin sojin da Faransa ke dauka a ƙasar Mali.

Karin bayani