An bullo da dokar takaita mallakar makamai a New York

Image caption Andrew Cuomo da Barack Obama

Jihar New York ta Amurka ta amince da daya daga cikin tsauraran dokokin mallakar bindiga kwana daya kafin Shugaba Obama ya bayyana shirinsa na takaita mallakar bindigogi a kasar.

Majalisar dokokin jihar ta gaggauta gudanar da sauye-sauyen ne bayan an kashe yara ashirin da shida da malamansu a wata makarantar firamare da ke jihar Connecticut a watan jiya.

'Yan jam'iyar Democrats da kuma wasu 'yan Republicans sun amince da matakan takaita yawan harsasan da za a sayarwa masu bindiga zuwa bakwa tare da bin diddigin tarihin mutanen da suke son sayen makamai.

Haka kuma an bullo da matakan tantance hankalin duk wanda ke son sayen bindiga.

Gwamnan NewYork, Andrew Cuomo, ya ce matakin ya nuna cewa masu kaunar zaman lafiya a kasar ne ke da rinjaye.

Karin bayani