Kungiyar 'yan aware za ta shiga yakin Mali

Image caption 'Yan tawayen Mali

Wani jami'in kungiyar Abzinawa 'yan aware wacce aka fi sani da MNLA a arewacin Mali ya ce a shirye suke su shiga yakin da ake yi da masu kaifin kishin Islama na kasar.

Da yake jawabi ga BBC jami'in, Moussa Ag Assarid, bai yi wani bayani dangane da ko kungiyar ta su za ta yi aiki tare da dakarun Faransa ba amma ya ce suna yakar kungiyar al-Qa'eda ne da 'yan ta'adda.

A yayin da Moussa Ag Assarid ke kokarin shiga yakin da ake yi da masu kaifin kishin Islama, ita kuwa gwamnatin Mali na kallon kungiyarsa a matsayin kungiyar 'yan ta'adda, kodayake ya musanta hakan

Kungiyar masu kaifin kishin Islamar dai ta kwace manyan biranen da ke arewacin Mali daga hannun kungiyar MNLA a bazarar ta ya wuce.

Karin bayani