Kazamin fada tsakanin sojin Faransa da 'yan tawayen Mali

Image caption Kasashe da dama na shirin tura dakaru kasar ta Mali

Jami'an tsaro a Mali sun ce sojojin Faransa da Mali na gwabza faɗa da dakarun 'yan tawaye a kan titunan garin Diabaly na yammacin Mali.

Masu kishin Islama ne suka ƙwace garin a ranar Litinin.

Kwanaki shida kenan jiragen yaƙin Faransa na lugudan wuta kan 'yan tawaye.

Shugaban Faransa Francois Hollande, ya ce ƙasarsa ta ɗauki matakin da ya dace, yana mai cewa, yin hakan ya zama wajibi.

Ya kuma ce, da an tsaya anatunanin yaushe za'a kai farmakin to da wankin hula ya kai dare.

Batun Mali a Nijar

A jamhuriyar Nijar ɗazu ne majalisar dokokin ƙasar ta soma wani zaman gaggawa na yini ɗaya, inda take tattaunawa akan buƙatar gwamnatin ƙasar na aike soja ɗari biyar zuwa ƙasar Mali domin yaƙar 'yan tawaye da suka ƙwace iko da mafi yawancin yankin arewacin ƙasar.

Nijar dai na daga cikin kasashe na farko da suka goyi bayan ra'ayin kungiyar ECOWAS na amfani da karfi domin kwato yankin arewacin na Mali.

Dukkan ɓangarorin majalisar dokokin Nijar sun bayyana goyon bayansu ga shirin aika dakarun zuwa Mali.