Charles Taylor ya bukaci da a biya shi fanshonsa

Charles Taylor
Image caption An ce Charles Taylor bai karbi kudaden fanshonsa ba tun 2003

Majalisar dattawan ƙasar Liberia ta samu wata wasika da aka ce ta fito daga tsohon shugaban ƙasar Charles Taylor, inda ya ke neman a biya shi kudaden fanshonsa na dala dubu 25 a kowacce shekara.

A yanzu haka Mr Taylor din na zaman wakafi ne na shekaru 50 kan aikata laifukan yaƙi, sai dai ya ɗaukaka ƙara.

Wasikar ta ce rashin adalci ne ganin cewa Mr Taylor bai karɓi fansho ba tun lokacin da aka tilasta masa barin mulki a shekara ta 2003.

Wakilin BBC a Liberia ya ce sa hannun da ke kan wasikar ya yi kama da na Mr Taylor, amma akwai wasu kura-kurai a rubutun da bai kamata a gan su a ciki ba.