Algeria: Wasu daga wadanda aka sace sun tsere

Masana'antar haƙar iskar gas a Algeria
Image caption Algeria na haƙo iskar gas ne tare da wasu ƙasashen waje

Kafofin yada labarai na Algeria sun bayar da rahoton cewa mutane goma sha biyar 'yan kasashen waje, da wasu talatin 'yan Algeria sun samu nasarar tserewa daga tashar iskar gas din da ake garkuwa da su.

Tun ranar Laraba ce dai wata kungiya mai alaka da kungiyar Al-Qa'ida take tsare da mutane da dama 'yan kasar waje da ma'aikata 'yan asalin kasar ta Algeria a tashar.

Har yanzu babu cikakken bayani a kan yadda mutanen suka tsere--kuma babu tabbaci a hukumance daga gwamnatocin kasashen da aka yi garkuwa da mutanensu.

Tun da farko dai rahotanni sun ce dakarun Algeria wadanda suka yiwa tashar gas din kawanya sun gwabza da masu tayar da kayar baya dauke da manyan makamai cikin dare.

'Yan kasashen wajen da ake garkuwa da su sun fito ne daga Burtaniya, da Faransa, da Amurka, da Norway, da kuma Japan.

Karin bayani