Al Shabab ta yi ikirarin kashe dan Kasar Faransa

Al shabab
Image caption Al Shabab ta yi ikirarin kashe Denix Allexx dan Faransa

Kungiyar masu kaifin kishin Islama dake Somalia, wato Al Shabaab tace ta kashe dan kasar Faransan nan da su ka yi garkuwa da shi shekaru hudu da suka gabata.

A wani sako da suka aike ta shafin Twitter, kungiyar ta Al Shabaab tace, ranar Laraba ne ta kashe Denis Allexx wanda jami'in leken asiri ne na Faransa.

Ranar Larabar da ta gabata ne dai wasu zaratan dakarun Faransa suka yi yunkurin kubutar da Denis Allex daga hannun Al Qaeda ba tare da samun nasara ba.

Yayin yunkurin dai an kashe sojan Faransa biyu da kuma 'yan Somalia goma sha bakwai.

Karin bayani