Kotun gaggawa zata saurari shari'ar zargin aikata fyade a India

Kotu a India
Image caption Shari'ar aikata fyade a India

Wato kotun majistre ta maida shari'ar da ake yiwa wasu maza biyar bisa zargin yiwa wata mace fyade a mota kirar bus a birnin Delhi zuwa wata kotu wacce take aikinta cikin gaggawa.

Matar 'yar shekaru ashirin da uku ta mutu ne sakamakon raunukan da ta samu bayan fyaden da ya harzuka jama'a musamman dangane da yadda ake muzgunawa mata a India.

Sai dai kuma tuni lauyan daya daga cikin wadanda ke fuskantar tuhuma V K Anand yayi korafin cewa zai daukaka kara

Ranar Litinin ne dai ake sa ran soma shari'ar.

Karin bayani