Kashin farko na sojin Najeriya sun tashi zuwa Mali

Major Janar S. U. Abdulkadir
Image caption Major Janar Abdulkadir ne zai shugabanci rundinar yaƙi da 'yan tawaye a Mali

Kashi na farko na sojojin Najeriya sun tashi da yammacin Alhamis zuwa Mali, inda za su bi sahun takwarorinsu na Faransa wadanda ke fafatawa da 'yan tawaye masu tsattsauran ra'ayin addinin Musulunci.

Kwamanda Mohammed Wabi na rundinar sojojin Najeriya ya shaidawa BBC cewa sojoji kusan tamanin ne suka tashi daga Kaduna zuwa ƙasar ta Mali, kuma gobe Juma'a wasu karin za su bi sahunsu.

Hakazalika ya ce a shirye suke don tinkarar aikin da ke gaban su a ƙasar ta Mali domin kuwa sun samu duk horon da suke buƙata.

Fiye da dakaru dubu uku ne daga ƙasashen Yammacin Afirka ake sa ran za su taka rawa a yunƙurin ƙwato arewacin Mali daga hannun 'yan tawayen.

Yanzu dai Najeriya ta kara yawan sojojin da ta yi alkawarin bayarwa zuwa dubu daya da dari biyu dakuma wasu jiragen saman yaki, maimakon dakaru dari tara da ta bayyana tun farko.

Wannan sabon adadi dai yana ƙunshe ne a cikin takardar da shugaba Goodluck Jonathan ya aikewa majalisar Dattawan ƙasar domin neman amincewarta a kan batun tura sojojin zuwa ƙasar ta Mali.

Karin bayani