'Matsalar 'yan gudun hijira na tsananta a Syria'

Image caption Ban Ki Moon

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa matsalar 'yan gudun hijira na kara tsananta a kasar Syria.

Ta ce mutane dubu uku ne ke komawa makwabtan kasashe a kowacce rana, kuma akasarinsu mata ne da kananan yara

Majalisar ta bayyana cewa ta yi rijistar 'yan gudun hijira kusan dubu dari shida da sittin, tana mai cewa adadin zai iya rubanyawa nan da tsakiyar shekarar da muke ciki.

Shugaban da ke kula da 'yan gudun hijira a yankin, Panos Moumtzis, ya bayyana wannan lamari a matsayin abin da ba a taba fuskanta ba.

Ya ce kudaden da aka bukata - dala miliyan dari biyar - don taimakawa masu gudun hijirar sun kusa karewa tun kafin su kai lokacin da aka kiyasta karewarsu.

Karin bayani