Munanan halayen 'yan tawayen Syria

Image caption Wani dan tawayen Free Syria Army

Rahotanni daga Aleppo, babban birnin Syria, sun nuna cewa mutane na kara fuskantar rashin kwanciyar hankali saboda munanan halayen da kungiyar 'yan tawaye ta Free Syrian Army ke nunawa.

Wakilin BBC da ke Aleppo ya ce 'yan kungiyar suna satar kayayyaki da kuma sace mutane domin karbar kudin fansa, lamarin da ke sa 'yan kasar na dawowa daga rakiyar su.

Kazalika hakan ya sa 'yan kasar suna kara bin ra'ayin kungiyar masu kaifin kishin Islama ta Nusra.

Tuni kungiyar ta Nusra ta kafa kotun shari'ar musulinci a Aleppo.

Daya daga cikin kwamandojinta ya shaidawa BBC cewa juyin juya halin da ake yi a kasar zai sa kasar ta zama mai bin tafarkin Islama sau da kafa.

Karin bayani