Algeria: An kuɓutar da 'yan kasashen waje 100

Image caption 'Yan kasashen waje da aka kuɓutar a Algeria

Kamfanin dillancin labaran Algeria ya ce zuwa yanzu an kuɓutar da mutane ɗari 'yan ƙasashen waje da aka yi garkuwa da su a wajen sarrafa iskar gas da ke arewacin ƙasar, inda masu kaifin kishin Islama suka mamaye a ranar laraba.

Kamfanin dillancin labaran ya ce har yanzu akwai 'yan ƙasashen waje talatin da ba a gano inda suke ba.

Amma hukumomin sun ce su na sa ran za a warware al'amarin cikin ruwan sanyi.

Wani ɗan Burtaniyan da aka kuɓutar ya bayyana jin dadinsa tare da jinjina wa sojojin Algeria yayin hira da gidan talabijin na ƙasar.

Akalla ma'aikata 'yan kasashen waje hudu ne suka mutu lokacin da dakarun Algeria suka kai hari matatar ranar Alhamis.

'Ba su da wata hujja'

Kawo yanzu babu "cikakken adadin wadanda ake tsare da su sannan rahotanni sun ce wasunsu sun nemi mafaka a wasu sassan matatar.

Fira Ministan Burtaniya David Cameron ya ce ya yi wa Algeria tayin gudummawar kayan aiki domin su fuskanci matsalar, sannan ya tuntubi shugabannin kasashen da abin ya shafi mutanensu.

Ya shaida wa majalisar dokokin kasar cewa yawan 'yan Burtaniya da ke cikin hadari ya ragu daga 30 kamar yadda aka ce tun da fari.

"Muna bukatar musan alhakin wanna abun a wuyan wa ya rataya, 'yan ta'adda su ke da alhakin wannan hari da salwantar rayuka. Ba su da wata hujja ta sace mutanen", a cewar Mr Cameron.

A yanzu dai ba a gudanar da aikin hakar gas din a matatar domin kaucewa hadarin fashewar gas.