Ghana ta miƙawa Ivory Coast Charles Goude

Image caption Charles Ble Goude, tsohon jagoran matasan Ivory Coast

Gwamnatin Ghana ta miƙa tsohon jagoran matasan Ivory Coast a lokacin tsohuwar gwamnatin Laurent Gbagbo ga hukumomin Ivory Coast bayan an masa tambayoyi a birnin Accra.

Jiya ne dai jam'ian tsaron Ghana suka cafke Mista Charles Ble Goude a wani gida dake birnin Accra.

Gwamnatin Alsan Oauttara ta Ivory Coast ce dai ta buƙaci gwmnatin Ghana da miƙa Charles Ble Gud wanda ake zargi da hannu a tashe tashen hankulan da aka yi a ƙasar ta Ivory Coast bayan zaƙen shugaban ƙasa da aka gudanar a cikin shekara ta 2010, inda a kashe mutane da dama.

Bayan zaɓen shekara ta 2010 ne dai ƙasar Ivory Coast ta tsunduma cikin rikicin da ya haddasa asarar rayuka da dukiya da dama.