Mali: an fattaki masu kishin Islama daga Konna

Image caption Sojan Najeriya a Mali

Sojan Mali sun ce sun sake karɓe iko da tsakiyar garin Konna, inda masu kaifin kishin islama suka ƙwace a farkon wannan watan.

Dakarun sojin Faransa da suka shiga cikin rikicin sun bude wuta a kudancin garin Diabaly.

Magajin garin Diabaly ya shaidawa BBC cewa a yanzu 'yan tawayen sun bar garin, sun nufi arewaci kusa da Timbuktu.

Sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da hakan.

Ministocin ƙasashen yankin yammacin Africa da takwaransu na Faransa Laurent Fabius sun fara wata tattaunawa a Abidjan don kula da matakin soji, kana shugabannin tarayyar Africa ta ECOWAS za su yi wata ganawar a gobe asabar.

Tu ni dai kashin farko na dakarun ECOWAS suka isa Mali, kuma Colonel Didier Dakouo yace sun samu kyakkyawar tarba daga al'ummar yankin.