'Yan bingida sun kai hari kan ayarin motocin Sarkin Kano'

Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero
Image caption Mutane da dama sun samu raunuka a harin

Rahotanni daga Kano a arewacin Najeriya sun ce wasu 'yan bindiga "sun kai hari kan ayarin motocin sarkin jihar Dr Ado Bayero, inda suka kashe akalla mutane biyar, cikin su har da direbansa da kuma dogaransa biyu da kuma Shugaban karamar hukumar Kumbotso.

Sai dai an ce Sarkin ya tsira da ransa, yayin da wasu da dama su ka samu raunuka ciki har da dansa Nasiru Ado Bayero - wanda shi ne Hakimin Tarauni.

Maharan sun bude wa tawaggar Sarkin wuta ne lokacin da yake barin masallacin Murtala bayan ya halarci saukar karatun Alkur'ani.

Dr Ado Bayero na daya daga cikin sarakunan gargajiyar da ke da karfin fada aji da kuma farin jini a arewacin Najeriya.

Birnin Kano ya sha fuskantar hare-haren 'yan bindiga wadanda a wasu lokutan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram ke daukar nauyi.

Sai dai kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin wannan harin na baya-bayan nan.

Wakilin BBC a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai ya bayyana cewa gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso ya tabbatar masa da aukuwar al'amarin, kuma ya shaida masa cewa tuni yaje ya gaida Sarkin, wanda yake cikin koshin lafiya.

Karin bayani