Dakarun Algeria sun kwace ikon matatar gas

Harin dakarun Algeria akan matatar gas na karshe
Image caption An kashe mutane da dama a matatar gas ta Algeria

Kasar Aljeriya ta ce dakarunta na musamman sun yi dirar maiki ta karshe a kan ma'aikatar iskar gas da ke cikin hamada, inda suka kashe 'yan fafitikar da suka kame ta, kuma sun kwace matatar.

Rahotannin Algerian na cewa dakarun kasar sun kutsa kai cikin matatar ne bayan da aka soma kashe wadanda akai garkuwa dasu

Har yanzu dai ba a san takamaimai mutane nawa aka kashe ba, amma akalla an ruwaito cewa an kashe akalla wadanda akai garkuwar da su sha tara da wasu 'yan bindiga talatin, tun lokacin da aka kwace matatar a ranar laraba

An dai sako daruruwan wadanda akai garkuwar da su bayan wani hari da sojoji su ka kai a ranar alhamsis

Kasashen yammacin duniya sun tabbatar da cewa an kawo karshen wannan aiki

Karin bayani