Dusar kankara na kawo cikas ga jiragen sama a Heathrow

Image caption Jama'a na jiran jirgi a Heathrow

Kamfanin sufurin jiragen sama na Brittaniya - British Airways ya nemi afuwa ga dubban fasinjojin da aka shirya tashinsu daga filin jirgin sama na Heathrow dake kusa da London saboda dagula tafiyar ta su da aka yi sakamakon dusar kankarar dake zuba ba kakkautawa.

Fasinjoji da dama sun shafe awoyi da dama a cikin jirage wadanda suka gaza tashi saboda rashin kyawun yanayi.

A ranar Jumm'a sai da aka soke tashin jiragen fiye da dari hudu; kuma aka rufe filin jirgin saman na Heathrow zuwa wani dan lokaci.

Wani mai magana da yawun kamfanin jiragen saman na British Airways ya ce, mai yiwuwa yanayin ya kara dagulewa a yau Assabar.