Shugabannin Afrika na ganawa a Abidjan

Image caption Sojan Najeriya a Mali

Shugabannin kasashen Afrika ta Yamma sun shirya ganawa yau Asabar a Abidjan dake Ivory Coast don tattauna yadda yakamata su tafiyar da aikin sojin da za a tura a kasar Mali.

Ana sa ran za su tattauna shirye-shiryen aikewa da sojojin na Afrika da za su tallafa wa sojojin Faransa da na Mali, wadanda yanzu haka suke fagen-daga.

Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ma zai halarci tattaunawar.

Wakilin BBC a yammacin Afrika ya ce wasu batutuwan da ake jujjuyawa sune na yadda sojojin na Afrika za su iya fafatawa da mayakan 'yan kishin Islama wadanda ke rike da manyan makamai.

A kasar ta Mali, jami'ai sun ce mayakan 'yan kishin Islama a yanzu sun fice daga garin Diablay na kudancin kasar wanda suka kwata a ranar Litinin a sakamakon ruwan bama-bamai da sojojin Faransa suka yi wa yankin.

Karin bayani