Gwamnatin Columbia ta gargadi FARC

Image caption Gwamnatin Columbia da FARC

Shugaban Columbia Juan Manuel Santos ya gargadi babbar kungiyar 'yan tawayen kasar watau FARC ta guji komawa kai hare-hare da za-ran wa'adin da aka gindaya na takaitacciyar yarjejeniyar dakatar da harin sari-ka-noke ta gama aiki a yau Lahadi.

Wakilan kungiyar ta FARC sun yi shelar tsagaita wuta tun farkon shawarwarin neman zaman lafiyar tare da gwamnatin Colombia watanni biyu da suka gabata.

To amma a na ta bangaren, gwamnatin Columbiar ta ki barin kai hare-hare na soji a lokacin shawarwarin, tana cewar 'yan tawayen masu ra'ayin kawo sauyi suna iya amfani da wannan damar su sake tara makamai.