Algeria: An gano wasu karin gawarwaki

Image caption Wadanda aka yi garkuwa da su a Algeria

Rahotanni daga Algeria sun ce sojojin dake binciken wurinda aka yi garkuwa da mutane a kamfanin sarrafa iskar gas na In-Amenas sun gano karin gawarwakin wasu mutane a kalla ashirin.

Akasarin su an yi musu harbi na fitar imani wanda sai a tsanake ne za a iya gane su.

Yanzu adadin wadanda aka kashe ya kai kimanin mutane tamanin.

Sai dai kuma ba a tantance ba ko su wane ne a aka gano an kashe sun; wadanda aka yi garkuwar da su ne ko kuwa 'yan kishin Islamar.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce an kashe mutanen da aka yi garkuwar da su arba'in da takwas.

Tun farko jami'an tsaron Algeria sun ce an kame mayakan 'yan kishin Islama su biyar da ransu, a yayinda ake neman sauran wasu su uku ruwa-a-jallo.

Wannan lamari da ya faru a In-Amenas ya jefa mutanen garin cikin damuwa.

Karin bayani