Gangnam Style ta jawo miliyoyin daloli

Gangnam Style
Image caption Gangnam Style ce wakar da aka fi kallo a tarihin You Tube

Kamfanin Google ya ce wakar Gangnam Style, wacce aka fi kalla a tarihin You Tube ta samar da kudaden shigar da suka kai dala miliyan takwas a You Tube din kawai.

A yanzu adadin wadanda suka kalli wakar ya kai biliyan daya da miliyan 250.

Kuma wanda yayi wakar wato Psy da kamfaninsa, za su samu dala miliyan hudu daga ciki.

Sai kuma....

Ba mamaki mallakar gida ya saukaka - saboda masana harkar zane a kasar Holland sun bayyana shirinsu na sabbin zane-zane na 3D.

Janjaap Ruijssenaars za su yi amfani da fasahar wurin yin kayayyakin gini kamar na katako da za a daure da kankare.

Za a samar da gidan farko a badi, amma sai mutum ya biya fan miliyan 3 da rabi ko kuma dala miliyan 5 da rabi tukunna.

Karin bayani