Sojojin Faransa sun shiga garin Diabaly

Image caption Masu fafutuka sun arce su bar garin Diabaly

Sojojin Faransa da na Mali sun shiga garin Diabaly, garin da masu fafutuka su ka kwace a makon daya gabata.

Rahotanni sunce jerin motocin yaki 300 da kuma sojoji fiye da 200 ne suka shiga cikin garin ba tare da sun fuskanci turjiya ba.

Rahotannin dai sun ce masu fafutukar sun arce sun bar garin ne a ranar Juma'a bayan da jiragen yakin faransa su ka yi musu luguden wuta na tsawon mako guda.

Faransa ta kaddamarda hari ne a Mali a makon da ya gabata domin kwace arewacin kasar da masu fafutuka su ka kwace.

Faransa ta tura dakaru dubu biyu ne Mali domin taimakawa sojojin kasar Mali domin yaki da masu fafutuka wadanda ake ganin suna da alaka da kungiyar Al'qa'ida.

Har wa yau Faransa ta yi kira ga kasashen yammacin Afrika da su gaggauta turo sojoji wadanda ake ganin yawansu zai kai dubu 3,000.