Sabon shafin musayar bayanai na Mega

Kim Dotcom
Image caption Kim Dotcom ne ya kafa shafin megaupload

Bayan da aka rufe daya daga cikin manyan shafukan musayar hotuna a internet -megaupload - a wani sumame a bara - mutumin da ya kafa shafin Kim Dotcom ya kaddamar da sabo.

"Mega" shafin ajiye bayanai ne kuma na baiwa masu amfani da shi damar ajiye bayanan da yawansu ya kai Giga Bite 50GB a kyauta.

Wannan a cewar masana shari'a, na nufin ba za a iya rufe shafin ba, idan aka yi amfani da shi ta hanyar da ta sabawa doka.

Kamar wurin musayar fina-finai da wakoki da manhajojin da ke da kariya.

A wani labarin kuma...

Idan kana da munanan hotuna a facebook - duk da cewa kusan kowa na da shi, ba mamaki a samu hanyar kawar da hotunan da mutum baya so.

Masana kimiyya a kasar Japan sun fito da gilasai da ke amfani da wata danja da za ta taimaka wurin gyara fuska.

Duk da cewa na'urar ba ta yin illa ga yadda mutum ke bayyana, ba mamaki ta nuna cewa ba kowa ba ne ke son fita tare da kai.