'Yan sanda a Thailand na sayar da 'yan gudun hijira

Image caption Rohingya musulmai, yan gudun hijira

Wani bincike da BBC ta gudanar ya nuna cewar Jami'an kasar Thailand da 'yan sanda wadanda suka baci da son kudi suna sayar da 'yan gudun hijira Musulmi Rohingya ga masu fataucin mutane.

Mayakan ruwan Thai sun cafke kananan jiragen ruwa da dama makare da su.

A wani lamarin guda, wata majiya dab da jami'an nan da son kudin ya yi wa kanta ta gaya wa BBC wasu 'yan gudun hijirar saba'in da uku da aka kame aka cika mota da su da nufin mayar da su gida, an mika su ne ga masu fasa-kwaurin mutane.

Wani mutum wanda yana cikin 'yan gudun hijirar da aka sayar ya gaya wa BBC cewar 'yan sanda ne suka sayar da shi ga masu fataucin mutanen wadanda suka rike shi a hannun su tsawon wata daya har sai da ya tara kudin da ya fanshi kan sa.

Karin bayani