An rantsar da shugaba Obama a karo na biyu

Barack Obama
Image caption Akwai dai gagarumin kalubale ga shugaba Barack Obama

Barack Obama ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Amurka karo na biyu a gaban dubban daruruwan 'yan kallo a birnin Washington DC.

Mr Obama, mai shekaru 51, wanda shi ne shugaban Amurka na 44, ya sha rantsuwa ne ta hannun alkalin alkalan kasar John Roberts.

Tun da farko an rantsar da shi a wani kwarya-kwaryar biki a fadar White House ranar Lahadi - tsarin mulkin kasar ya ce wajibi ne shugaba ya fara aiki ranar 20 ga watan Janairu.

Shugaba Obama ya shaida wa mahalatta taron cewa ya dau ranstuwa ne da sunan Ubangiji da kuma kasar - ba wai da sunan jam'iyya ba.

Ya ce a yanzu mataki ya rage na mu, kuma ba za mu bata lokaci ba. Bai kamata mu yi wasa da ikon da aka bamu ba, ko saka siyasa cikin muhimman batutuwa na kasa.

"Bari mu tashi tsaye domin tabbatar da tarihi," a cewar Obama lokacin da yake kammala jawabin na sa.

A fitaccen dakin taron nan na Blue Room tare da matarsa da kuma 'ya'yansa mata biyu, shugaban ya dora hannunsa akan littafin Bible na mabiya addinin Kirista wanda iyalan Michelle Obama suka shafe shekaru suna amfani da shi, a lokacin da yake karbar rantsuwa daga mai shari'a Roberts.

Bikin rantsuwar dai ya hada da kada-kade da wakoki, inda mawakiyar nan Beyonce ta rera taken kasar Amurka a karshe.

Karin bayani