Sudan ta Kudu ta kori manyan hafsoshin sojin ta

Shugaba Silva Kiir na Sudan ta Kudu
Image caption Sudan ta Kudu ta kori wasu manyan hafsoshin sojin ta

Shugaba Sudan ta Kudu Silva Kiir ya kori manyan hafsoshin sojin kasar guda shidda tare da maye gurbinsu da wasu.

Haka kuma Hafsan Hafsoshin sojin kasar ya raba wasu janar-janar guda talatin da mukamansu, aka mayar da su sojin jiran-tsammani.

Matakin, wanda ake gani a matsayin wanda ya fi tsananin tun bayan samun 'yancin kasar ya dan tada hankali, inda ake ta kila-wa-kala game da sha'anin tsaro kasar.

Ministan watsa labarun Kasar ya fadawa BBC cewa gwamnatin Kasar ta dauki wannan mataki ne da zummar sanya sabbin jini a rundunar sojin Kasar.

Karin bayani