An sauya dokar fyade a Morocco

Morocco
Image caption Kungiyoyin mata sun yi marhabin da dokar fyade

Kungiyoyin mata a Kasar Morocco sun yi marhabin da matakin da gwamnati ta dauka na cire dokar da ta baiwa mutanen da ake zargi da yiwa kananan yara fyade, damar barin gidan yari idan su ka auri matan da su ka yiwa fyaden.

Sai dai sun ce matakin farko ne kawai a yunkurinsu na ganin an sauya dokokin da basa kare hakkin mata daga cin zarafi a kasar ta Morocco.

An yi wannan yunkuri ne shekara guda da ta gabata bayan wata budurwa 'yar shekara 16 Amina al-Filali, ta kashe kanta sakamakon tilasta mata da aka yi ta auri mutumin da ya yi mata fyade.

Mutumin dai ya yi amfani da dokar ce wacce ta baiwa wadanda aka samu da laifin cin hanci ko satar kananan yara su fita daga gidan yari idan suka auri wadanda suka ci zarafin.

Karin bayani