Korea ta Arewa ta bijire wa Majalisar Dinkin Duniya

Kasar Korea ta Arewa
Image caption Kasar Korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta mai da martanin da ke bijirewa kudurin Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, da ya kara tsaurara takunkumin da aka kakaba mata.

Wata sanarwa da ta fito daga Ma'aikatar Harkokin waje a Pyongyang ta ce kasar za ta kara karfin sojinta, ciki har da makamanta na nukiliya.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar dai, ya kada kuri'un Allah-wadai ne da kaddamar da roka mai cin dogon zango da kasar ta Korea ta Arewa ta yi kwanan baya.

Ya kuma yi barazanar daukar matakai idan Pyongyang tayi yunkurin gwajin makaman nukiliyar.

Shugaban kwamitin sulhun , Masood Khan ya bayyana cewa baki ya zo daya wajen amincewa da daftarin kudurin a matsayin Kudurin Majalisar Dinkin Duniyar na shekara ta 2013.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Susan Rice ta ce 'yan kasar Korea ta arewa su san cewar ana lura da duk wani takun su.

Miss Rice tace wannan kudiri ya nuna wa kasar Korea ta Arewa cewa, akwai sakamakon da ka iya biyo bayan karya dokokin shawarar da kwamitin ya yanke.

Kudirin dai ya biyo bayan yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Amurka da kasar China, babbar kawar kasar Korea ta Arewar.