Rahoton kungiyar Amnesty a kan Kamaru

Amnesty International
Image caption Amnesty ta yi zargin Kisa da gallazawa jama'a a Kamaru

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta wallafa wani rahoto game da Kamaru.

Rahoton ya shafi yawan kisa da gallazarwar da ake yi wa jama'a - ciki har da 'yan siyasa hadi da manema labaru a kasar.

Kungiyar ta kuma bada misali da yawan cunkoson jama'a da ake samu a gidajen kurkukun Kasar

Wallafa wannan rahoton ya biyo bayan ziyarar aikin da wani jami'in Kungiyar ya kai Kamaru ne, inda ya gudanar da bincike.

Karin bayani