Pakistan na tsare mutane ba tare da gurfanar da su ba

Jami'an tsaron Pakistan
Image caption Kungiyar Amnesty ta zargi Pakistan da azabtarwa

Pakistan, a karon farko, ta amsa cewa tana tsare da wadanda ake zaton masu fafitika ne ba tare da ta gurfanar da su a gaban shari'a ba.

Wakiliyar BBC ta ce, "Ministan Shari'ar Pakistan din, Irfan Qadr, ya sheda wa Kotun Kolin kasar cewa za a ci gaba da tsare su har sai an kawo karshen farmakin da soji ke kaiwa a kan 'yan kungiyar Taleban."

Sai dai Babban Mai Shari'ar Pakistan, Iftikar Muhammad Chaudry, ya ce kamata ya yi a yi masu shari'a, ba wai a tsare su ba kan ka'ida ba.

Amnesty International ta zargi Pakistan da tsare dubun dubatar maza da yara maza, kuma da dama daga cikin su, an azabtar da su, zargin da Pakistan ta musanta.

Karin bayani