Masar: Ana tarzomar adawa da gwamnati

Image caption Masu tarzoma a Masar

Dubban masu zanga-zanga na bijirewa 'yan sanda a dandalin Tahrir da ke birnin Alƙahira na ƙasar Masar a rana ta biyu ta zagayowar cika shekaru biyu da juyin-juya halin da ya hamɓarar da gwamnatin Hosni Mubarak.

Tuni dai aka soma yin arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro.

Su dai masu zanga-zangar suna zargin gwamnatin Muhammad Morsi da jam'iyyarsa ta 'yan uwa musulmi da kaucewa manufofin juyin-juya halin da aka yi a ƙasar.

Sai dai kuma tuni Pray minista, Hisham Qandil ya maida martani da cewa, gwamnati tana buƙatar lokaci domin aiwatar da sauye-sauye ta fuskar siyasa da tattalin arzikin.

Tun daga bayan hamɓare gwamnatin Mubarak ne kasar ta Masar ke cigaba da fuskantar tarnaƙin siyasa.