Rundunar Sojin kasar Mali na gudanar da bincike

Sojojin kasar Mali
Image caption Sojojin kasar Mali

Rundunar Sojin kasar Mali ta ce tana gudanar da bincike kan zargin da ake yi cewa sojojin gwamnati sun aikata kashe-kashe na ba gaira ba dalili.

Wani babban jami'i ya shaidawa BBC cewa rundunar ba za ta tabbatar ko ta musanta faruwar kashe-kashen ba.

Wata kungiyar kare hakkin bil-adama ta kasa da kasa, mai helkwata a birnin Paris ce ta yi zargin jami'an sojin da aikata kisan, yayin fadan da suke yi da mayaka masu tsattsauran kishin Islama.

A ranar Larabar da ta gabata ne kungiyar ta ce, a rahotannin da ta samu an kashe akalla mutane goma sha daya a wani sansanin soji a garin Sevare, yayin da aka kashe wasu ashirin a kusa da wurin.

Wani jami'i a rundunar sojin Faransa ya ce ba su da masaniya a kan wannan al'amari sai dai a kafofin yada labarai.

Yace da sun ga wani abu mai kama da haka na faruwa tabbas da sun sanar da shugabanninsu nan take.

Yanzu haka dai an samu karuwar mutanen da suka rasa matsugunansu a kasar, yayinda suke ci gaba kauracewa rikicin dake neman daidaita kasar.

Mata da dama a sansanin 'yan gudun hijira dake garin Djenni, tsakiyar kasar ta Mali sun ce sun bar gidajensu domin tsira daga fadan da ake gwabzawa, amma kuma suna fuskantar matsaloli na halin zaman rashin tabbas.