Amurka ta yi nazari kan manufofinta - Kerry

Sanata John Kerry
Image caption Mr John Kerry na jawabi gaban kwamitin tsara manufofin gwamnatin Amurka kan kasashen waje

Mr John Kerry, wanda shugaba Barack Obama ya tsayar a matsayin sabon sakataren harkokin wajen Amurka , yayi kiran a yi sabon nazari kan manufofin gwamnati.

Tsohon dan majalisar dattawan jam'iyar Democrat din na bayyana hakan ne yayinda yake jawabi ga kwamitin tsara manufofin gwamnati kan asashen waje.

Kwamitin dai shine wanda zai yanke shawarar tabbatar masa da mukamin ko kuma akasin hakan.

Mr Kerry ya kuma ce dole ne batun tattalin arzikin Amurka ya zama shine kan gaba, domin sahihancin huddar diplomasiyyar Amurkar.

Ya kuma ce manufofin gwamnati kan kasashen waje ba su kasance kan aikewa da sojoji ko jiragen yakin da basu da matuka ba kadai, har ma da batutuwan damuwa kamar su shirin samar da abinci, da shawo kan matsalar sauyin yanayi.

Mr Kerry ya jinjinawa Mrs Hilary Clinton, wacce zai maye gurbinta, game da gagarumin aikin da ya ce ta yi.