Majalisar Dinkin Duniya za ta kara sojoji a Congo

Dakarun jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo
Image caption Dakarun jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo

Jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun za su kaddamar da wata runduna da za ta yaki kungiyoyi 'yan tawaye a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.

A cewarsu, rundunar wacce ba a kai ga amincewa da ita ba, za ta taimakawa rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, da a yanzu haka aka dorawa alhakin kare fararen hula a kasar ta Congo.

Jami'an aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniyar sun ce yanzu haka ana gab da kammala shirin aikewa da karin sojoji kimanin dubu biyu da dari biyar.

Sojojin za su gudanar da aikin kare fararen hula, da kuma hana kungiyoyin 'yan tawaye kwace wasu yankunan kasar.

Jami'an sun ce, za a yi amfani da jiragen yakin da basu da matuka, don taimakawa sabbin dakarun da aka aike gabashin Congo wajen sa ido kan dakarun 'yan tawayen.

Kwace garin Goma da 'yan tawayen M23 suka yi a karshen bara ne ya haddasa daukar wadannan matakai.

A wancan lokacin, dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ba su kalubalancin 'yan tawayen ba wadanda ke dauke da manyan makamai, al'amarin da ya sa kimarsu ta zube.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya sha matsa kaimin ganin cewa an yi hattara sosai wajen tunkarar rikicin dake faruwa a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, da sa hannun wasu kasashe makwabta, dama rashin mayar da hankalin gwamnati da dakaru kasar ta Congon.