Dakarun kasar Masar na yin sintiri a birnin Suez

Dandalin Tahrir a birnin Alkahira, kasar Masar
Image caption Dandalin Tahrir a birnin Alkahira, kasar Masar

Dakarun kasar Masar na yin sintiri a birnin Suez, bayan kashe akalla mutane takwas, yayin zanga-zangar da aka gudanar a fadin kasar.

Babban jami'in hukumar tsaro na Suez Adel Refaat, ya ce ya gayyato sojojin ne don su taimaka wajen shawo kan tashe-tashen hankulan dake faruwa a kasar.

A rana ta biyu ta cika shekaru biyu da kifar da gwamnatin Hosni Mubarak, dubban masu zanga-zanga ne suka bayyana adawarsu da Shugaba Muhammad Morsi da jam'iyyun masu kishin Islama wadanda suka zarga da karkatar da akalar juyin juya-halin kasar.

Likitoci a kasar ta Masar sun ce akalla mutane biyar ne aka bindige har lahira a birnin na Suez, lokacin da ake yin artabu tsakanin masu zanga-zangar adawa da gwamnati, da kuma jami'an tsaro.

An kuma samu fadace-fadace a bisa titinan biranen Askandaria da Port Sa'id, dama wasu biranen.

Masu zanga-zangar dai sun zargi kungiyar 'yanuwa musulmi ''Muslim Brotherhood'', da shugaba Mohammed Morsi da karya alkawuran da suka yi na juyin juya halin.

Dubun dubatar masu zanga-zangar ne suka hallara a dandalin Tahrir dake birnin Alkahira, suna bayyana dalilan da suka sa suka shiga cikin zanga-zangar.

Shugaba Morsi dai ya yi kira da a kawo karshen tashin-tshinar, amma kuma an ci gaba da arangama har cikin dare a kofar Ma'aikatar cikin gida a birnin Alkahira.