Mutane talatin ne suka rasu a Port Said

Masu zanga zanga a Masar
Image caption Masu zanga zanga a Masar

Rahotanni daga Masar na cewa an kashe akalla masu zanga zanga 16 a tarzomar da ta barke tsakanin 'yan sanda da masu zanga zanga a garin Port Said, biyowa bayan hukuncin kisan da wata kotu ta yanke wa mutane 21 da aka kama da laifi a tashe tashen hankulan da akai tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa a shekara ta 2012.

Iyalan wadanda suka mutun a wannan lokaci sun yi ta suwwa a cikin kotun lokacin da suka ji hukuncin da aka yanke musu.

Sai dai kuma ana bayyana hukuncin iyalai da magoya bayan mutanan da aka yankewa hukuncin su kai yi kokarin kutsa kai cikin gidan yarin da ake tsare da su.

Inda daga nan kuma wasun su suka fantsama kan tituna suka fara zanga zanga. Suna nuna cewa kotun ba ta yi adalci ba.

Rahotannin sun ce an yi arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga zangar a birnin Port Said, a lokacin da suke kokarin tsarwatsa masu zanga zangar.

Wasu majiyoyi a wani asibiti dake birnin sun ce akalla mutane talatin ne suka rasa rayukansu , ciki har da 'yan sanda biyu da 'yan wasan kwallon kafa biyu, yayin da sama da mutane dari uku kuma suka samu raunuka.

Yanzu haka dai an tura sojoji garin na Port Said domin tabbatar da kwanciyar hankali.

Fadan da akai bara tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa na Port Said da wani daga birnin Alkahira ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 70.

Inda aka zargi 'yan sanda da rashin yin wani abun aza a gani wajan dakatar da rikicin.

Karin bayani