Fada tsakanin 'yan tawaye a Pakistan

A Pakistan akalla mutane talatin da hudu ne yawancinsu yan tawaye suka rasa rayukansu daga ranar juma'a zuwa yau a cigaba da arangamar da ke faruwa tsakanin kungiyoyin yan takifen da ke gaba da juna a yankin kan iyaka da Afghanistan.

Fadan ya barke ne tsakanin yan Taliban na Pakistan da kuma kungiyar Ansarul Islam wadda ke goyon bayan gwamnati bayan da kungiyar Taliban ta Pakistan ta kame wasu wuraren binciken ababen hawa a kwarin Tirah.

Sai dai kuma kungiyar Ansarul Islam ta yi Ikrarin kwato wuraren.

Kwarin dai yana da matukar muhimmanci saboda ya hade mashiga zuwa Afghanistan da kuma Pakistan.