Neman zaman lafiya a Kudancin Sudan

Majalisar samar da zaman lafiya da tsaro ta kungiyar gamaiyar Afirka ta bayar da wasu jerin shawarwari da nufin kawo karshen rikici a kudancin Sudan inda gwamnati ke yaki da yan tawaye a kudancin Kordofan da kuma wasu lardunan Blue Nile.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dubban daruruwan jama'a a wurin suna bukatar taimakon jin kai a sakamkon rikicin.

Majalisar zaman lafiyar ta kungiyar gamaiyar Afirka ta bukaci tsagaita kai hare hare domin bada damar shigar da kayayyakin agaji, ta kuma yi kiran gudanar da tattaunawa kai tsaye tsakanin gwamnati da yan tawaye.

Majalisar dai na son ganin bangarorin biyu sun fara tattaunawa domin samun masalaha ta lumana kafin sha biyar ga watan Fabrairu mai kamawa.

Sai dai kuma a wata hira da ba kasafai ya kan yi ta ba, shugaban yan tawayen ya shaidawa BBC cewa kamata ya yi a fara gabatar da taimakon jin kan al'umma kafin a fara dukkan wata tattaunawa.