Daruruwan dalibai ne suka mutu a Brazil

'Yan uwan mutanan da suka mutu a Brazil
Image caption 'Yan uwan mutanan da suka mutu a Brazil

Akalla mutane 230 --- yawancin su dalibai--- ne suka rasa rayukansu a wata gobara da ta tashi a wani gidan rawa a kudancin birnin Santa Maria.

Kafafan yada labarai na cikin gida sun ce wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce gobarar ta tashi ne da tsakaddaran lahadi bayan da wata kungiyar makada ta fara wasannin tartsatsin wuta sai wayar lantarkin da aka sa a cikin bangon ta kama da wuta.

Rahotanni sun ce gidan rawar na da kofa daya ne kacal an kuma sami firgici da rudewa yayin da mutane suka yi ta kokarin ficewa,kuma yawancin

Yanzu haka 'yan uwan wadanda suka rasun sun fara duba gawarwakin mutanansu a dakin motsa jikin da akai amfani da shi wajan ajiye gawarwakin.

Sama da mutane dari ne yanzu haka ke kwance a wasu asibitocin dake kusa, inda ake kula da su.

Wata likita a asibitin garin Santa Maria ta ce mutane da dama sun yi dafifi a gaban asibitin suna jiran bayanai akan 'yan uwa da abokansu.

Tuni shugabar kasar Brazil din Dilma Rousseff ta soke dukka tarukan da take da su a wajan taron kolin kasashen yankin Latin Amurka da ake a Chile, sakamakon wannan gobara.

Kuma yanzu haka ta je garin na Santa Maria, inda ta nuna matukar alhininta cikin tausayi a lokacin da ta ke ganawa da 'yan uwan wadanda gobarar ta ritsa da su.

Daga nan kuma ta ratsa daya daga cikin asibitocin da ake kula da wadanda suka ji raunuka.

Karin bayani