An takaita fita a wasu birane a Masar

Masar
Image caption An shafe kwanaki uku a jere ana tarzoma a birane da dama a kasar ta Masar

Shugaban kasar Masar Muhammed Morsi ya bada sanarwar kafa dokar ta baci a biranen Port Said, da Suez da Ismailia.

Dokar za ta yi aiki ne na kwanaki 30 tare kuma da takaita zirga-zirga daga karfe 9 na dare zuwa 6 na safe agogon kasar.

Tun da farko an bada rahoton cewa mutane uku sun rasu wasu daruruwa kuma sun sami raunuka a tashe tashen hankula a birnin Port Said a lokacin da ake jana'izar akalla mutane talatin din da aka kashe yayin wata arangama a ranar Asabar.

'Yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa dubban masu zaman makoki wadanda yawancin su har yanzu suke cikin fushi da hukuncin kisa da kotu ta yankewa wasu mutane ashirin da daya dangane da rawar da suka taka a mummunan tarzomar da ta biyo bayan kwallon kafar da aka yi a birnin a bara.

A birnin na Alkahira an rufe ofisoshin jakadancin Birtaniya dana Amurka na wucin gadi sakamakon tarzomar da ke cigaba da faruwa.

Karin bayani