Sojojin Faransa a Mali sun kwace 'Gao'

Ma'aikatar tsaron kasar Faransa ta ce sojojin kasar da na Mali da sun kwace garin Gao da ke arewacin kasar Mali.

A baya dai yan tawaye ne masu kaifin kishin Islama tare da hadin gwiwar yan tawayen abzinawa su ka kwace garin a watan Afrailun bara.

Sojojin Faransa ne su ka fara shiga garin, bayan da su ka kwace filin saukar jiragen sama da ke garin da kuma wata muhimmiyar gada dake kudu da garin.

Jami'an kasar Faransa dai sun ce sojoji kasashen da dake makwabtaka da Mali wato Niger da Chadi ne za su shiga cikin garin domin tabbatar da doka da oda.

Har wa yau Faransa ta ce tana kokarin ganin cewa an dawo da gwamnatin a garin kuma tuni ma Magajin garin na Gao ya dawo bayan da aka kori yan tawayen.

Har yanzu dai ba'a san adadin mutanen da su ka rasa rayukansu ba a Yunkurin kwace garin, amma wani jami'in Sojin Mali ya ce an kashe yan tawaye da dama kuma babu sojan Faransa ko kuma na Mali da ya rasa ransa a bata kashin da aka yi.