Sojoji a Mali na fatattakar 'yan tawaye

Sojojin Faransa a Mali
Image caption Sojojin Faransa a Mali

Sojojin Faransa na cigaba da dannawa birnin Timbuktu dake hamadar sahara a arewacin Mali wanda yan tawaye masu kaifin kishin Islama suka kwace a watan Aprilun bara.

Wani wakilin BBC a Mali yace akwai kyakkyawan zato sojojin Faransa za su karbe Timbuktu cikin sauki.

Tun a yan kwanakin da suka wuce ne dai runduna mai yawa ta sojojin suka dumfari arewacin kasar ta Mali.

Akwai yiwuwar za su cigaba da yin luguden wuta akan garin domin sharar fage.

Wannan matakin dai ya zo ne kwana guda bayan da hadin gwiwar sojojin Faransa dana Mali suka kwace birnin Gao inda yan tawayen ke da karfi.

Batun na Mali shine zai mamaye jadawalin taron kolin kungiyar gamaiyar Afirka a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha.

Karin bayani